Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsaro: Buhari Ya Kira Taron Gaggawa


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Facebook/Femi Adesina)
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Facebook/Femi Adesina)

Hukumomin tsaron Najeriya sun ce suna daukan matakan da suka dace wajen ganin sun dakile duk wata bazarana da ka iya tasowa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi taron gaggawa da manyan jami’an tsaron kasar a Abuja a ranar Litinin.

Wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar a karshen mako, ta ce taron zai mayar da hankali ne kan yadda za a karfafa matakan tsaro a sassan kasar.

Taron zai wakana ne kwanaki bayan da Amurka ta fitar da wata sanarwa da ke cewa akwai yiwuwar akai hare-hare a wasan sassan Najeriya, ciki har da Abuja babban birnin kasar.

Rahotanni sun ce, Amurkar ta kwashe wasu daga cikin jami’an diflomasiyyarta da iyalansu da ke Abuja.

Hukumomin tsaron Najeriya sun ce suna daukan matakan da suka dace wajen ganin sun dakile duk wata bazarana da ka iya tasowa.

Najeriya, wacce ita ce kasar da ta fi yawan al’uma a nahiyar Afirka, na fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga da Boko Haram a arewaci da kuma matsalar ‘yan aware a kudanci, ko da yake mahukuntan kasar sun ce lamarin na lafawa.

XS
SM
MD
LG