Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Goyon Bayan CBN Kan Shirin Sauya Fasalin Kudinmu - Buhari


Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

“Mutanen da suka binne haramtattun kudade a karkashin kasa, su ne za su fuskanci kalubale idan muka yi hakan.”

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya amince babban bankin kasar na CBN ya yi sauye-sauyen a wasu daga cikin kudaden takardu na kasar.

Buhari wanda ya fadi hakan cikin wata hira da ya yi da fitattun ‘yan jarida Halilu Ahmed Getso da Kamaluddeen Sani Shawai da harshen Hausa, ya kara da cewa shirin zai taimakawa kasar a fannoni da dama, kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar ta ce.

“Shugaba (Buhari) ya ce dalilan da CBN ya zayyana masa kan bukatar yin sauye-sauyen, za su taimaka wajen rage hauhawar farashin kayayyaki da rage jabun kudade da ke yawo a hannun mutane da kuma rage yawan kudade a tsakanin al'uma.” Sanarwar ta kara da cewa.

“Mutanen da suka binne haramtattun kudade a karkashin kasa, su ne za su fuskanci kalubale idan muka yi hakan, amma ma’aikata da ‘yan kasuwa da ke samun kudaden shiga ta hanyoyin halal, ba za su fuskanci wata matsala ba.” Buhari ya fada a hirar.

Buhari ya kara da cewa, ba ya ganin adadin wata uku da aka diba don gudanar sauye-sauyen ya yi kadan kamar yadda wasu suke fada.

A makon da ya gabata, babban bankin na CBN a Najeriya ya sanar da shirin sauya fasalin wasu daga cikin kudaden kasar na takardu.

Cikin wata sanarwa da bankin ya wallafa a shafukan sada zumunta a karshen makon da ya gabata, CBN ya ce sauye-sauyen za su shafi takardun Naira 1,000, 500 da kuma 200, ba dukkan kudaden kasar ba kamar yadda ake ta yadawa bisa kuskure.

XS
SM
MD
LG