Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guguwar Harvey Ta Fara Yin Sauki A Yanken Jihar Texas


Jami'an agaji da na tsaro sun ceto fiye da mutane 13,000 daga gidajensu sakamakon ruwan sama da guguwar Harvey.

Ana sa ran ruwan sama na tarihi da ake yi a garin Houston dake jihar Texas zai dan tsagaita yau Laraba, yayinda muguwar guguwar Harvey ke janyewa daga gabashin jihar, ta nufi jihar Louisiana.

Kwararru na hasashen cewa garin na Houston zai sami ruwan sama mai yawan santimita 2 yau Laraba kuma rana zata fito, sannan za a yi zafi zuwa ranar Jumma’a. Sai dai yankin zai cigaba da fama da ambaliyar ruwa sakamakon ruwan saman da zai cigaba da sauka, wanda ya zuwa yanzu ya zubda fiye da santimita 130 na ruwan a wasu wurare tun daga ranar 24 ga watan nan na Agusta.

A gabashin Houston kuma, a garin Beaumont, duk a jihar ta Texas, an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a safiyar yau Laraba yayinda guguwar ta nufi Louisiana. Hukumar dake sa ido akan ruwan sama da guguwa ta kasa, ta ce za a yi ruwa mai yawan santimita 15 zuwa 30 a kudu maso yammacin jihar Louisiana yayinda guguwar ke kara shigowa ciki-ciki.

Jami’an yanken da na jihar Texas sun ce ma’aikatan agaji sun ceto fiye da mutane 13,000 daga gidajensu da suka cika da ruwa, kuma dubban mutane na cibiyoyin tsugunnar da wadanda ambaliyar ta shafa a wani ginin gwamnati dake birnin na Houston, da kuma filin wasan kwallon kwando, na birnin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG