Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Yi Alkawarin Farfado Da Tattalin Arzikin Amurka


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi jawabinsa bayan amincewa da sake tsayawa takara a hukumance domin neman wa'adin mulki na biyu karkashin tutar jam'iyar Republican

Attajirin mai harkar gidaje kuma fitaccen mai gabatar da shirin a gidan talabijin, Donald Trump wanda a lokutan baya, da yawa daga cikin masu jefa kuri’a suke kallonsa a matsayin wani wanda ba’a sani ba a siyasa, lokacin da ya fito takar shugaban kasa a 2016, ya amince a hukamce da sake tsayawa takara karo na biyu karkashin tutar jam'iyar Republican

A lokacin tsayawa takararsa ta farko, masu sharhi da binciken jin ra’yoyin jama’a sun hakikanta cewa zai fadi zaben shugaban kasa, amma Trump ya lashe zaben ya kada Hillary Clinton ‘yar jam’iyyar Demokrat, kuma yanzu ya sake dawowa neman wani wa’adin mulki.

A cikin jawabin da ya gabatar daga Fadar White House, Trump ya bayyana cewa ya cika alkawuran da ya yi a lokacin yakin neman zabe shekaru uku da rabi da suka shige, ya kuma ce idan aka sake zabensa, zai dora a kan nasarorin da ya samu.

Ya ce "na tsaya a wannan dare a gaban ku da jin dadin goyon baya da ku ke bani, ina alfahari da irin cigaba da muka samu a cikin shekaru hudu da su ka gabata kuma ina fatan za mu cigaba da gina Amurka a cikin shekaru hudu masu zuwa."

Trump ya ce zai sake dawo da tattalin arzikin Amurka wanda ya ce shine mafi girma a duniya, idan masu jefa kuri’a sun amince ya ci gaba da zama a Fadar White House.

Shugaban Amurkan ya ce,“Mun yi da farko, kuma yanzu ma za mu sake yi,” Sannan wannan lokaci, zamu karasa aikin.​

Ya kara da cewa a shekaru uku da rabi na mulkinsa, an rage kudin haraji da ya dadadawa Amurkawa ya kuma taimaka a fannin harkarkokin kasuwancin Amurka da daidaikun su.

Trump yace suna alfahari da gina Katanga a tsakanin Amurka da kasar Mexico domin hana kwararowar bakin haure wanda ya bayana cewa Mexico bata biya ko mai ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG