Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Joe Biden Ya Yi Alkawarin Shawo Kan Annobar Coronavirus


Joe Biden
Joe Biden

Bayan shafe kusan rabin karni a fagen siyasar Amurka, a jiya Alhamis da daddare, Joe Biden ya amince da ya zama dan takarar shugaban kasar Amurka a zaben 3 ga watan Nuwamba,

A cikin jawabinsa bayan amincewa da tsayawa takara, Biden ya gayawa Amurkawa lokaci ya yi da za’a kawar da shugaban kasa Donald Trump bayan ya yi wa’adi daya a fadar White House.

“idan muka hada hannu za mu ga bayan wannan mummunan lokaci,” a cewar Biden yayin da Amurka ta ke fuskantar matsalar barkewar annobar coronavirus kana miliyoyin ma’aikata Amurkawa suka rasa ayyukasu. Ya kuma yi alkawarin shawo kan wadannan matsalolin idan ya zama shugaban kasa,

Ya bayyana cewa, Trump bai dauki nauyin yadda cutar ta yadu ba, ya kuma ki jagoranci.

Joe Biden yana jawabin amincewa da tsayawa takara
Joe Biden yana jawabin amincewa da tsayawa takara

Biden yace, “duk tsawon lokacin da aka dauka, har yanzu wannan shugaban bashi da wani shirin yakar annobar. Ya gaza kare Amurkawa, ba a a lamunci wannan ba.”

Jawabin na Biden, da ya yi daga dakin taro na garin Wilmington na jihar Delaware, ya zo ne a ranar ta hudu kuma dare na karshe na babban taron jam’iyyar Demokrat da ya hada da jawabai da aka nada ta kafar bidiyo, da kuma wadanda aka gabatarwa kai tsaye da suke yabawa Biden da kuma caccakar shugabancin Trump na shekara uku da rabi.

Trump da yan Refublikan za su maida martani a taronsu na kasa na kawaki hudu da za’a fara ranar Litinin. Amma Trump, a ziyarar da ya kai jiya Alhamis zuwa Old Forge, a jihar Pennsylvania da Biden ya fito, ya nuna irin yadda ‘yan Refublikan zasu caccaki Biden.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG