Lamarin dai ya samo asali ne daga ikirarin da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya yi na cewa, ba a da hurumin gurfanar da shi a gaban kotu a kan kokarin da ya yi na sauya sakamakon zaben shugaban kasa na 2020 da ya nuna ya sha kaye, da ya kai ga gungun magoya bayansa da suka kutsa kai cikin Majalisar Dokokin kasar tare da kawo cikas ga tabbatar da zaben shugaba Joe Biden.
Mafi tasirin hukuncin nan da nan shi ne cewa, kusan ya ba da tabbacin cewa ba za a yanke hukunci kan tuhume-tuhumen da gwamnatin tarayya ke yi kan yunkurin kifar da zaben shugaban kasa na 2020 ba kafin zaben 2024, da Trump ke takara karkashin tutar jam’iyar Republican. Idan har ya ci zabe, zai iya sa a yi watsi da karar gaba daya.
Abin jira a gani shi ne yadda wannan hukunci zai shafi yadda shugabannin da za su gudanar da rayuwarsu a yayin da suke kan karagar mulki, sai dai masana da dama sun ce matakin na iya bude kofar wuce gona da iri.
Alkalan kotun shida masu ra'ayin mazan jiya ne da su ke da rinjaye, suka fitar da ra'ayin da babban mai shari'a John Roberts ya rubuta, a rana ta karshe ta tsawaita wa'adin, yayin da alkalai masu sassaucin ra'ayi guda uku suka yi allah-wadai da wannan matsayin.
Alkalan mafiya rinjayen dai sun kawar da yiwuwar tuhumar Trump kan wasu abubuwa da ya yi bayan zaben da suka hada da yi wa jami’in ma’aikatar shari’a barazanar kora daga aiki sai dai idan ya yi karyar cewa hukumar na binciken yiwuwar magudi a wasu jihohin da suka zabi Biden.
Sai dai sun bar yuwuwar cewa masu gabatar da kara za su iya kalubalantar kariyar a kan wadansu ayyukan da ya gudanar a matsayin Shugaban kasa, suka bar kananan kotuna su yanke wannan shawarar.
Dandalin Mu Tattauna