Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Musanta Cewa Tattaunawar Amurka Da China Ta Wargaje


A wani al'amari mai kama da neman yayyafa ruwa ma al'amarin da ya zafafa, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce har yanzu Amurka da China na tuntubar juna, duk kuwa da cewa an samu baraka a tattaunawar baya.

Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta cewa tattaunawar da ake yi tsakanin Amurka da China da zummar warware takaddamar kasuwanci ta wargaje, kuma ya na bayyana al'amarin, wanda akasari Ake kira yakin-kasuwanci tsakanin kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya, da “dan rashin fahimtar."

"Ana kan tattaunawa. Kuma har kullum za a cigaba da yi," in ji Trump, lokacin da yake amsa tambayoyin Muryar Amurka a farfajiyar kudu ta fadar White House, a jiya Talata. Ya kara da cewa, "Saura kiris mu cimma jituwa sai kawai su ka saba."

A sakamakon haka, jami'an gwamnati sun ce Shugaban na Amurka, a wannan makon, ya yanke shawarar zurfafa abin da suka fito kiri-kiri su ka kira: yakin kasuwanci da cinikayya tsakanin Amurka da China.

"Ba wanda kan yi nasara a yakin kasuwanci da cinikayya," in ji shugaban Majalisar Dattijai Mitch McConnell, lokacin da yake ganawa da manema labarai, bayan jawabin Trump. Ya ce, "Muna fatan wadannan matakan za su sa mu cikin yanayi mai kyau."

Facebook Forum

Shugaba Donald Trump ya ba gwamnatinsa damar tasa keyar bakin haure daga kasar, da kai wasu kurkuku na Guantanamo Bay dake Cuba
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 3:00 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Shehu Kanam mai sharhi kan al’amura ya mana karin bayanin matsayin dalilan yawaitar fashewar tankokin man fetur a Najeriya
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 4:23 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Karin haske akan dalilan dake kawo aukuwar haduran tankar mai a Najeriya da musabbabin karuwar wannan lamari a baya-bayan nan
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 4:37 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG