Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Kare Kansa Game Da Korar Daraktan Hukumar FBI


Trump
Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya kare kansa game da matakin da ya dauka na sallamar daraktan hukumar bincike ta FBI James Comey, yana cewa, “Ai baya aikinsa ne da kyau. Illa iyaka”

Trump yayi wannan furuci ne a ofishinsa a jiya Laraba a lokacin da yake tare da tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Henry Kissinger.


Kafin nan Trump ya fadi a shafinsa na kafar Twitter cewa kowani dan Republican da dan Democrat da ke Washington ya yanke kauna ga Comey.


A cikin jerin sakwannin Tweeter da ya dora a shafinsa, Trump yace wanda za a nada madadin Comey, zai yi aiki mai inganci ya dawo wa hukumar FBI mutuncinta da darajarta.


Shima mataimakin shugaban kasa Mike Pence ya kare matakin shugaban a jiya Larabaya da cewa Trump ya dau matakin da ya dace kuma a daidan lokacin da ya dace.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG