Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Ta Horas da 'Yan Jarida daga Kasashe 18


Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson

Daga kasashe 18 ne Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta tattaro wasu 'yan jarida zuwa nan Amurka inda ta basu horo a Jami'ar North Carolina ta Chapel Hill da daya daga jihar Texas

Bayan an basu horon an shirya masu rangadin wasu jihohin kasar domin bude ido tare da kara fahimtar abubuwan da suka koya.

Kasashen 18 an zabosu ne daga nahiyoyin Afirka da Asiya da Pacifi da gabashin Turai tare da kasar Larabawa.

Baicin kara masu ilimi akan aikin jarida sun kuma samu kwarewa akan harkokin tattalin arziki da siyasa da tsaro da zamantakewa irin na Amurka. Sun samu zarafin ganawa ta keke da keke da wasu kososhin gwamnatin Amurka.

Yawancin wadanda suka samu horon sun lura da yadda tattalin arzikin Amurka ya ta'allaka akan masana'antun kowane mataki ba lallai manya ba.

Wadanda aka tattauna dasu sun bayyana irin karuwar da suka samu musamman akan mahimmancin kananan masana'antu.

Yar jaridar da ta fito daga Daular Larabawa tace da ta dauka tattalin arzikin Amurka ya ginu ne akan manyan masana'antu bata san kananan na taka muhimmiyar rawa ba.

Ga sauran rahoton da Hasssan Maina Kaina ya aiko.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:48 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG