Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Indonesia: An Yankewa Gwamnan Jakarta Hukuncin Shekaru Biyu Saboda Yiwa Musulunci Batanci


Gwamnan Jakarta, Basuki Tjahaja
Gwamnan Jakarta, Basuki Tjahaja

An yanke hukuncin daurin shekaru biyu a gidan sarka akan gwamnan jihar Jakarta ta Indonesia, wanda Kirista ne, bayanda aka same shi da laifin yi wa Musulunci batanci, a wata shara’ar da ake ganin kamar babbar jarabawar ce ta farko da ake wa akidar jurewa zama da juna a kasar.

Wannan hukuncin daurin, wanda akace ya ma zarce tsawon lokacinda lauyoyin da suka shigar da karar suka nema, yana zuwa ne kamar Wata daya bayan da Basuki Tjahaya Purnama, wanda ake wa lakabin Ahok, ya sha kasa a rumfunan zabe, a kokarin da yayi na ci gaba da zama kan mukaminsa na gwamna.

Tun cikin watan Disambar bara ne dai aka gurfanarda gwamnan a gaban kotu a bisa zargin cewa yayi ta batanci akan addinin Islama a lokacinda yakin neman zabe a kusa da birnin na Jakarta, wanda shine babban birnin kasar.

Ance a lokacin ne ya karanto wata Aya ta Alkur’ani don nuna cewa ba inda aka hanawa Musulmi zaben wand aba Musulmi ba.

Bayanda maganar tashi ta bazu a duniyar gizo ne, abin ya janyo cece-kucce da tarukkan zanga-zanga, inda aka yi ta sukan lamirinsa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG