Ministan tsaro da kuma Shugaban Sojojin Afghanistan sun ajiye mukamansu biyo bayan mummunan harin da aka kai akan wata babbar barikin sojojin wanda yayi sanadiyyar mutuwar akalla sojoji 140 da kuma jikkata wasu da dama.
Kungiyar Taliban itace ta dauki alhakin wannan mummunan hari akan Bataliyar Soji ta 209 mai suna Shaheen Corps dake Arewacin birnin Mazar-e-Sharif.
A wata gajeriyar sanarwa ofishin Ghani yace “Ministan Tsaro Abdullah Habibi da kuma Shugaban Sojoji Staff Qadam Shahim sun ajiye mukamansu nan take” kuma shugaban kasa ya karbi saukar tasu.
Daga baya Habibi tare da Shahim sun fadawa taron manema labarai cewa sun sauka ne da kansu ba wai tilasta musu aka yi ba.
Facebook Forum