Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar Takarar Shugabancin Kasar Faransa Marine Le Pen Ta Canza Matsaya


Marine Le Pen
Marine Le Pen

Wuni daya bayan ayyanata a matsayin yar takara da zata je zagaye na biyu da Emmanuei Macron mai matsakaicin ra’ayi, Marine Le Pen mai kishin yan kasa da kyamar baki ta fada cewar zata janye a matsayin shugaban jami’iyarta amma ta zama ‘yar takara shugaban kasar yan Faransa baki daya.

A wani matakin fadada kimarta ga masu zabe, Le Pen ta fada a wani shirin Telbijin na kasar ta Faransa jiya dare, cewa, daga wannan dare ni ba yar takarar jami’iyar National Front bace. Tace ni yar takarar shugabancin kasa ce kawai, ta kara da cewar zata ajiye siyasar jami’iya a gefe daya.

Masu fashin baki suna kallon wannan mataki a matsayin wannan kalubale a siyasar kasar Faransa. Le Pen ta samu kashi 21.5 cikin dari na kuru’un zaben shugaban kasa a yayin da Macron ya samu kashi 23.8 cikin dari na kuru’un. Masu takarar suna bukatar cikakken rinjayi kafin su yi nasara a zaben zagaye na biyun da za a gudanar a ranar bakwai ga watan Mayu.

Wannan shi ne karon farko a tarihin Faransa a wannan zamanin, da wani wanda ba dan takarar wata dadaddiyar jam'iyya ba, zai - ko za ta - zama Shugaban kasa, wanda hakan ke nuna irin tsananin tsanar hukumomin kasar da ake yi, wanda hakan kuma zai yi tasiri kan ko Faransa za ta cigaba da kasancewa mambar Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ko kuma ta bi sahun Burtaniya wacce ta fice da kuma tafarkin Amurka karkashin Donald Trump.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG