‘Yan takarar shugabancin kasar Faransa guda biyu sun kaddamar da kamfe a yau Litinin domin neman kuri’u masu yawa, ta hanyar nunawa masu zabe cewar suna da hanyoyin sauya Faransa da suke bukata.
Zabin da ke gaban masu kada kuri’a a Faransa a zagaye na karshe da za’ayi a ranar 7 ga watan Mayu zai kasance kodai Faransa ta zauna a cikin kungiyar tarayyar turai ko kuma tabi sahun Birtaniya na barin dangi.
Zaben tsohon ma’aikacin banki kuma ministan tattalin arziki, Emmanuel Macron da kuma ‘Yar kishin kasa Marine Le Pen, ya nuna yadda masu zabe suka yi watsi da abinda aka saba gani a harkokin siyasar Faransa , abinda masu sa ido suka ce wani juyin juya hali ne a harkokin siyasar Faransa . A karon farko tun Jamhuriya ta biyar ta Charles de Gaulle an yi watsi da masu sassaucin ra’ayi zuwa masu tsatstsauran ra’ayi na jam’iyyar Republican daga takara baki daya.
Facebook Forum