Ya zuwa yanzu kayan taimakon da Amurka da wasu kasashen suka aika basu kai ga mutanen Venezuela ba, a don haka kayan na jibge ne a wasu garuruwa cikin Colombia da Brazil da kuma Curacao.
Shugaban Venezuela Nicholas Maduro da ake jayayya da shi yace ba a bukatar taimakon ya kuma ce taimakon ya sabawa doka.
Kasar Venezuela tana fama da karancin abinci da magani da wasu abubuwan rayuwa na yau da kullum kana tana fama da tsananin tsadar rayuwa fiye da duk wata kasa a duniya. Mutane miliyan uku da suka kai kashi goma cikin dari na al’ummar Venezuela sun arce daga kasar.
Facebook Forum