Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Bijirewa Matsayar Taron G-7


Shugaban Amurka, Donald Trump a taron kolin kasashen G-7 da aka kammala a Canada
Shugaban Amurka, Donald Trump a taron kolin kasashen G-7 da aka kammala a Canada

Shugaba Donald Trump ya bijirewa matsayar da aka cimma a taron kolin kasashen da suka fi karfin tattalin arziki na G-7 da aka kammala a Canada.

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce ya bai wa wakilansa umurnin cewa kada su rattaba hannu a wata takardar matsaya da aka cimma, a tsakanin kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki na G-7 wanda aka yi a Canada.

Trump na nuni ne da sanarwar da Firai Ministan Canada Justin Trudeau ya fitar bayan da shi Trump din fice daga taron kolin.

A wani sakon Twitter da ya wallafa a shafinsa, Trump ya kuma kwatanta sanarwar ta Trudeau a matsayin “mai rauni wacce ke cike da rashin gaskiya.”

Firai Ministan na Canada ya rufe taron ne a jiya Asabar, inda ya ki amincewa ya sauya matsayar da ya dauka ta nuna adawa da harajin da Amurka ta sakawa kayayyakin karafa da dalma na kasarsa ta Canada da na kasashen da ke nahiyar turai.

A jawabin rufe taron, Trudeau, ya bayyana cewa zai dauki matakan maida martani kan matsayar saka harajin da Amurka ta dauka, akan kayayyakinta, nan da ranar 1 ga watan Yuli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG