Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Ce Yana Iya Gayyatar Shugaban Koriya ta Arewa Zuwa Fadarsa


Donald Trump, shugaban Amurka
Donald Trump, shugaban Amurka

A cewar shugaban Amurka Donald Trump ya ce idan taron kolinsu da shugaban Koriya ta Arewa ya tafi dede yadda ake zato, yana iya gayyatar shugaban Kim Jong Un zuwa Fadar White House

Shugaban Amurka Donakd Trump ya fada jiya Alhamis cewa, zai gayyaci shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un, ya kawo ziyara Amurka idan komi ya tafi yadda ake so a taron kolin da zasu yi da zai shiga tarihi. Amma a daya gefen a shirye yake ya fice daga taron idan bai gamsu da abunda ke gudana ba.

Shugaba Trump yayi wata ganawa ta tsawon sa'o'i biyu da Firayi Ministan Japan Shinzo Abe a jiya Alhamis din a fadar White House kasa da mako daya gabannin taron kolin. Abe ya nemi tabbacin Amurka na ganin an sami ci gaba wajen shawo kan shirin Nukiliyar Korita ta Arewa,KTA da makamai masu linzami da kuma batun 'yan kasar ta Jaspan da take zargin KTA ta sace su a wajajen 1970 da kuma da 1980.

A taron manema labarai na hadin gwuiwa da suka yi bayan ganawar, Mr. Trump yayi alkawarin zai kawo batun a lokacin taron kolin shi da Mr. Kim Jong Un.

Ahalinda ske ciki kuma, kwanaki gabannin taron kolin tsakanin Amurka da KTA, wakilan majalisar dokokin Amurka 'yan Republican sun bayyana goyon bayan su ga yunkurinn da shugaba Trump yake yi.Su kuma 'yan Jam'iyyar Democrats sun bayyana damuwa kan taron kolin, sun kara da cewa hakan ba yana nufin suna fatan ganin shugaban na Amurka ya gaza ba ne. Wasu sanatoci 'yan Republican suka ce bin tafarkin difilomasiyya na tunkarar rikicin na Nukiliya itace hanyar da zata hana Amurka yaki da kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG