A daren jiya Laraba, zababben shugaban Amurka Donald J. Trump ya zabi Kari Lake ta jagoranci Muryar Amurka (VOA)
Iina farin cikin sanar da cewa Kari Lake ce za ta zamo daraktar Muryar Amurka mai zuwa,” ya bayyana a cikin wata sanarwa.
Ms. Lake, tsohuwar mai gabatar da shirye-shirye a kafar yada labarai ta Phoenix, a cewa Trump, za ta yi aiki tare da mutumin da zai jagoranci kafar yada labaran Amurka da ake sauraro a duk duniya wanda nan bada jimawa ba za’a bayyana sunansa domin tabbatar da cewar an yada muradan Amurka, ciki har da na fadin albarkacin baki yadda ya kamata.
Ms Lake ta yi martani da cewa “karramawa ce da Shugaba Trump ya bukace ne in jagorancin Murya Amurka.”
Ta kara da cewa Muryar Amurka wata kafar yada labaran kasa da kasa ce mai muhimmancin gaske da aka ware domin yada manufofin Amurka ta hanyar tattaunawa kai tsaye da al’ummomin duniya tare da dabbaka akidun dimokiradiya da gaskiya, mai masu sauraron da yawansu ya kai mutane miliyan 354.
Muryar Amurka na yada labarai cikin harsuna 49. A karkashin jagoranci na, Muryar Amurka za ta yi zarra kan manufarta: ta yada nasarorin Amurka a fadin duniya.”
Dandalin Mu Tattauna