Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Da Harris Sun Yi Allah Wadai Da Zanga-Zangar Kin Jinin Isra'ila, Shugaba Biden Ya Gana Da Netanyahu


Pro-Palestinian demonstrators protest near the US Capitol before Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu addresses a joint meeting of Congress on July 24, 2024, in Washington.
Pro-Palestinian demonstrators protest near the US Capitol before Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu addresses a joint meeting of Congress on July 24, 2024, in Washington.

Zanga-zangar na zuwa ne a daidai lokacin da Firai ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ke kare yakin da kasar ke yi a Gaza, a yayin jawabi da ya yi a zauren Majalisar dokokin Amurka.

Manyan ‘yan takarar shugabancin Amurka biyu, mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris da tsohon shugaban kasa Donald Trump, sun ya yi Allah wadai da zanga-zangar nuna adawa da Isra'ila wacce aka fara ranar Laraba a kusa da ginin majalisar dokokin Amurka.

Harris Da Trump
Harris Da Trump

Zanga-zangar na zuwa ne a daidai lokacin da Firai ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ke kare yakin da kasar ke yi a Gaza, a yayin jawabi da ya yi a zauren Majalisar dokokin Amurka.

Harris, wacce ta yiwu ita ce ‘yar takarar shugaban kasa ta jam’iyyar Democrat a zaben shekarar nan ta 2024, a cikin wata Sanarwa ta ce "Mun ga ayyukan Allah wadai daga marasa kishin kasa masu zanga-zanga da munanan kalaman kiyayya a tashar jirgin kasa ta Union Station da ke kusa da ginin majalisar dokoki."

ISRAEL-PALESTINIANS/USA-NETANYAHU-PROTESTS
ISRAEL-PALESTINIANS/USA-NETANYAHU-PROTESTS

A gaban tashar, masu zanga-zangar sun cire tutocin Amurka suka sanya Tutocin Falasdinawa, sannan wani mutum ya yi amfani da jan fenti ya rubuta “Hamas na nan tafe" da manyan harrufa a kan wani babban sassake. Bayan haka Masu zanga-zangar sun kona wani mutum-mutumi na Netanyahu da tutar Amurka.

Shi ma Trump, ya rubuta a shafin sa na sada zumunta na Truth cewa “Idan da wadanda suka ta da tarzoma jiya a Washington ‘yan Republican ne, da yanzu dukkansu na tsare a gidan yari, suna fuskantar hukuncin dauri na shekaru 10 zuwa 20. Amma a karkashin wannan Gwamnatin, babu abin da zai same su."

A jiya Alhamis Shugaban Amurka Joe Biden ya karbi bakuncin Firai Minista Benjamin Netanyahu a fadar White House, don tattaunawa da nufin ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma sakin sauran mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su, tun bayan harin da ta kai kan Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoban bara.

Shugabannin biyu sun gana a Ofishin shugaban kasa, kwana daya bayan da dukkansu sun gabatar da muhimman jawabai. A ranar Laraba Netanyahu ya yi magana a gaban Majalisar Dokokin Amurka, inda ya kare yakin da kasarsa ke yi da mayakan Hamas.

Shi kuwa shugaba Biden ya yi jawabi game da dalilin da ya sa ya yanke shawarar janyewa daga takarar shugaban kasa a ranar Lahadin da ta gabata, tare da bayyana goyon bayansa ga mataimakiyarsa.

Shugaban Amurka Joe Biden Da Benjamen Netanyahu
Shugaban Amurka Joe Biden Da Benjamen Netanyahu

Dukkan shugabannin biyu sun gabatar muhimman jawabai a takaice kafin ganawar da suka yi ta sirri.

To sai dai gabanin ganawar, wani babban jami'in gwamnatin kasar ya shaidawa manema labarai cewa shugabannin biyun suna aiki kan cikakkun bayanai game da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma sakin wadanda aka yi garkuwa da su, "wadda suka ce sun yi imani ana a matakin karshe."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG