Ficewar Shugaba Biden daga takarar shugaban Amurka ta 2024, tasa ya zama daya daga cikin shugabani kalilan da suka shude da suka dakatar da kamfe din sake neman takara.
Sai dai janyewar Biden ta zo a makare, fiye da yadda wani dan takara daya shude yayi lokacin da yake kan karagar mulki.
A ‘yan makonnin baya-bayan nan, Biden ya nace akan cewar zai ci gaba da kamfe duk kuwa da damuwar da aka rika nunawa akan shekarunsa dama lafiyar kwakwalwarsa.
Sai dai bayan kiraye-kiraye da tsaffin magoya baya da masu fada a ji a jam’iyyar democrats, shugaban kasar ya janye a jiya Lahadi 21 ga watan yulin da muke ciki, ana kasa da watanni 4 a gudanar da zabe.
Babu wani shugaban kasar dake neman a sake zabarsa daya taba janyewa a makare haka.
Shugaban amurka Harry S. Truman, bayan daya shafe akasarin shekarun wa’adin mulkinsa guda 2 (bayan ya cancanci sake tsayawa), ya janye daga takarar 1952 a karshe watan maris, bayan daya gaza samun rinjayen kuri’u a zaben fidda gwanin jam’iyyar democrat na jihar New Hampshire a farkon watan.
Daga bisani Shugaban Amurka Lyndon B. Johnson ya janye daga takara a zaben 1968 shima a karshen watan maris, sakamakon karancin goyon baya.
Akwai wasu shugabannin kasar da dama da suka yanke shawarar fasa takarar neman wa’adi na 2, duk da cewar sun sanar da hakan ne gabanin kaddamar da gangamin yakin neman zaben. James K. Polk da James Buchanon da Rutherford B. Hayes da Theodore Roosevelt da Calvin Coolidge dukkaninsu sun sanar da wuri cewar ba zasu nemi sake yin takara ba, inda wasu suka sanar da aniyarsu tunda fari, ko kuma tun a lokacin kamfe din neman wa’adi na farko.
Wadanda basu sanar da aniyarsu ta kin sake tsayawa takara da wuri ba-irinsu Roosevelt da Coolidge-sun gaji shugabancin kasar ne bayan mutuwar tsaffin shugabannin kasar sannan suka sake cin zabe da kansu (kamar dai yadda truman da johnson suka yi)
Akan batun Roosevelt, ya sha alwashin cewar ba zai nemi wa’adi na 3 ba sa’ilin da yake yakin neman zaben wa’adinsa na 2-saidai yayi takara a 1912, inda a karshe Woodrow Wilson ya kada shi. Coolidge ya sanar a watan Agustar 1927 cewar baya sha’awar shiga zaben 1928, inda yayi ikrarin cewar, wa’adi na 2 ya yiwa shugaban kasa tsayi.
Kari akan wadannan sunaye na sama, akwai kuma wadansu shugabannin Amurkan wadanda bayan shafe wa’adin mulkinsu na 2 (George Washington da Thomas Jefferson) suka ki amincewa su nemi wa’adi na 3, duk kuwa da cewar sun cancanci yin hakan.
(Gyaran kundin tsarin mulkin amurka na 22, wanda ya zama doka a 1951, ya kayyade wa’adin mulkin shugaban kasa)
Biden, duk da cewar ya fi dukkanin shugabannin Amurka da zayyano sunayensu a sama janyewa daga takara a makare, ya baiwa jam’iyyarsa ta Democrat lokacin da zata gudanar da gangami, tare da fidda sunan sabon dan takara a hukumance.
Saidai, hakan, wani lamari ne mai zaman kansa.
Dandalin Mu Tattauna