A jiya Litinin ne ‘yan majalisar dokokin Amurka suka yi kira ga Daraktar da ta yi murabus, yayin da take ba da shaida kan gazawar hukumar wajen hana yunkurin kashe dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donald Trump.
Kwanaki tara bayan yunkurin hallaka Trump, lamarin da ya girgiza al'ummar kasar, an samu amsoshi kan yadda mai harbin ya samu kusanci da Trump.
A karon farko dai Shugabar Hukumar tsaron farin kaya Amurka Kimberly Cheatle, ta amsa tambayoyin 'yan majalisar game da harbin, inda tace, "hakika Mun gaza."
Cheatle ta ce za a fitar da cikakken rahoton hukumar a cikin kwanaki 90. Sai dai ‘Yan majalisar sun ce hakan bai dace ba, sabili da a lokacin zabe ne, zaben da ke cike da rudani.
-AP
Dandalin Mu Tattauna