Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Takarar Shugaban Kasar Amurka Sun Tafka Muhawara


Muhawarar Trump da Biden
Muhawarar Trump da Biden

Shugaban kasar Amurka na jam’iyyar Republic Donald Trump da abokin takararsa na jam’iyyar Democrat tsohon shugaban kasa Joe Biden, sun tafka muhawara a daren jiya Talata.

Nan da nan da fara muhawarar suka fara caccakar junansu kan yadda ya kamata a shawo kan annobar coronavirus a Amurka, wadda yanzu tafi kowacce kasa a duniya yawan wadanda cutar ta kashe,inda sama da mutum 205,000 suka mutu.

Biden ya fada cewa “Shugaban kasa bashi da wani shiri,” Ya ci gaba da cewa “Ya san cutar mummuna ce, kuma yaki fadawa mutane hakan.”

Shugaba Trump dake neman wa’adi na biyu bayan lashe zaben 2016, ya maida martani da cewa “Mun yi aikinmu da kyau. Nan da ‘yan makonni rigakafi zata samu.”

Shugaba kasa ya zargi Biden da kiransa makiyin baki, sabili da ya takaita shigowa daga kasar China, inda cutar ta samo asali.

Muhawarar da ta kwashe mintuna 90 a kwaleji dake birnin Cleveland na jihar Ohio, na zuwa ne makonni biyar kafin zaben ranar 3 ga watan Nuwamba. Ita ce karon farko cikin uku da ‘yan takarar biyu zasu yi, baki daya ‘yan takarar shekarunsu ya wuce 70, kuma zasu sake fuskantar juna a muhawarar da za a yi wata mai zuwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG