Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Fara Bada Maganin Rigakafin Coronavirus A Ranar Litinin


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Amurka ta tabbatar da bukatar gaggawa na afmani da maganin rigakafin coronavirus kana maganin zai fara isa ga mutane da safiyar gobe Litinin a fadin Amurka.

Wannan wata gagarumar nasara ce ga kasar da COVID-19 ta hallaka sama da mutum dubu 295, a cewar cibiyar nazarin cutar coronavirus ta jami’ar John Hopkins.

Shugaban shirin samar da maganin rigakafi na gwamnatin Trump "Operation Warp Speed," Janar Gustave Perna, ya fada a taron manema labarai a jiya Asabar cewa kamfanonin aika kaya zasu fara kai zubi miliyan uku na maganin rigakafi da Pfizer ya yi zuwa ga cibiyoyin raba maganin 150 na kasar kana wasu karin cibiyoyi 450 zasu samu maganin kafin ranar Laraba.

Da yammacin ranar Juma’a ne hukumar kula da abinci da magunguna ta FDA ta tabbatar da rigakafin da kamfanin Pfizer ya yi tare da takwararsa na kasar Jamus, BioNTech bisa bukatar gaggawa.

Ma’aikatan kiwon lafiya da gidajen duban tsofaffi ne zasu fara samun maganin a cikin zubi miliyan uku na farko.

Shugaban hukumar abinci da maguguna Stephen Hahn ya fada a taron manema labarai a jiya Asabar a wajen Washington cewa shima kansa zai sha maganin da zara an fitar da shi.

Hahn ya yabawa aikin tabbatar da ingancin maganin, inda ya ce shine mafi sauri a tarihin tabbatar da rigakafi a Amurka, ya kuma ce hukumar sa bata bada muhimmanci ga yin sauri fiye da inganci ba.

Hahn ya karyata labarin da aka yada a ranar Juma’a cewa shugaban ma’aikatan fadar White House Mark Meadows ya yi barazanar tsige shi idan bai tabbatar da maganin rigakafin ba zuwa wani kayyadadden lokaci.

XS
SM
MD
LG