Dan wasan gaba na Tottenham da kuma kasar Ingila Harry Kane zai tafi jinya har zuwa wata mai zuwa bayan sakamakon rauni da yaji a idon sawunsa a gasar cin kofin Premier a ranar Lahadi tsakaninsu da Bournemout.
Kungiyar ta Tottenham tabada tabbacin haka ne bayan an duba kafar dan wasn a ranar litini, dan haka Harry Kane, bazai buga wasan da kungiyar zata yi da swansea city, ba a wasan Dab da na Kusa da na karshe na cin kofin kalu bale na kasar Ingila ranar asabar.
Haka kuma ba zai fafata a wasannin sada zumunta da kasarsa ta Ingila zata yi ba a wannan satin, Kuma wannan ba shine karon farko da dan wasan ya taba samun irin wannan raunin ba a shekarar da ta gabata ya rasa wasanni 10 sakamakon irin wannan rauni.
Harry Kane, a bana ya zurara kwallaye 35 a wasanni daban daban da ya buga wa kungiyar Tottenham, Kane 24 ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na twitter cewar zai yi duk abinda zai iya yi domin komawa buga wasanni.
Kocin kungiyar Manchester united, Jose Mourinho zai Gana da manya manyan jami'an kungiyar kan batun kasafin kudin da za'a kashe a lokacin hada hadar saye da sayarwa na shekara mai zuwa, sai dai ana ganin kungiyar PSG, ta kasar faransa tana barazanar daukansa da ya koma gareta a a shekara mai zuwa.
Facebook Forum