Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FIFA Ta Fitar Da Kashin Farko Na Tikitin Shiga Kallon Wasannin Cin Kofin Duniya


Cikin awoyi 24 na fari, hukumar kula da kwallon kafa ta duniya ta bada umurnin fara sayar da tikiti guda 365,700 na shiga kallon wasan cin kofin duniya da za a buga a kasar Rasha na shekarar 2018, a shafin ta na yanar gizo mai adireshi FIFA.com/tickets.

Za a fara sayar wa masoyan kwallon kafa dake kasar Rasha, sai na Amurka guda, da Agentina da Colombia sai Mexico, da Brazil sai Peru, da kasar Australia, da Jamus da China sai India wannan tikiti.

Duk ta yawan bukatar tikitin da ake da kuma tsaikon samun sa a yanar gizo, hukumar ta ba masoya kwallon kafa shawarar shiga shafin kai tsaye domin ganin yadda zata kasance da kuma lokacin da zasu iya sharewa suna jira kafin su samin tikitin.

Daga karshe hukumar ta bada bayanin cewa babu wata kafa ko shafin yanar gizo da mai bukatar tikitin wasan zai iya samun sa sai ta shafinta na yanar gizo kamar yadda yake a rubuce a farko.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG