Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta cika kwallayenta na dubu daya a raga a gida bangaren gasar Firimiya lig ta kasar Ingila.
Kungiyar ta samu wannan nasarane ta kafar dan wasan gabanta Shkodran Mustafi, a wasan da suka yi da Watford, ranar Lahadi wasan mako na 30 a Firimiyr bana.
Shkodran Mustafi, ne ya jagoranci kungiyar ta Arsenal a kwallon farko cikin mintuna takwas da fara wasan da taimakon Mesut Ozil, inda daga karshe aka tashi 3-0 bayan Aubameyang da Mkhitaryan, sun jefa nasu kwallayen.
Kungiyar Arsenal ta kasance kungiya ta biyu cikin jerin kulob din da suka fi zurara kwallaye a gida a bangaren firmiya lig, Manchester united ce kasance ta daya wace ta zuba kwallaye har 1066, a gidanta a tarihin gasar ta Firimiya lig ta kasar Ingila.
Facebook Forum