Bisa ga al’ada a kasar Pakisatan, kowace sana’a tana da wanda ake danganta ta, kamar sana’ar kwallon kafa an san maza da wannan sana’ar, ko kuma duk wata sana’a da ta shafi aikin karfi, wasu kuwa ana danganta su da sana’ar mata.
Shahnaz Kamal, mace daya mai kamar maza, domin kuwa ta dauki sana’ar da ake dangantawa da maza ta maida ta sana’arta, ita ce mace daya kuma ta farko a tarihin kasar da take Koyar da matasa masu sha’awar damben Boxing.
Wannan mata ta sami lasisinta na koyar da damben Boxing, ga matasa, ta kwashe shekaru 2 tana koyon danben na kwararru, wanda ta samu goyon baya daga mijinta, ta zama mace ta farko mai rike da kambun 3-star a baki daya kasar ta Pakistan.
Ta bude makarantar koyar da damben boxing ga matasa, wanda take cewa “Tana mamakin yadda gwamnatoci basu taimaka ma mata masu sha’awar wasan boxing, amma hakan bai sa ta yi kasa a gwiwa ba, wajen ganin ta taimaka ma ‘yan uwanta mata ba”.
Duk kuma da rashin isassun kayan koyarwa na zamani, bata karaya ba, ya zuwa yanzu tana da dalibai mata da maza da suke da sha’awar wasan, kuma zata cigaba da taimaka musu don cinma burin su na yau da kullun.
Ta kara da cewar, ya kamata gwamnatoci da masu hannu da shuni, su taimaka wajen karfafa ma mata da matasa gwiwa wajen shiga wasan kai tsaye.
Facebook Forum