Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Umarci Ministoci, Shugabannin Soji Su Rage Adadin Motocin Da Ke Ayarinsu


Shugaba Bola Tinubu (Hoto: X/Bayo Onanuga)
Shugaba Bola Tinubu (Hoto: X/Bayo Onanuga)

Daukar wannan mataki a cewar Fadar Shugaban kasar, yunkuri ne na rage kudaden da gwamnati ke kashewa.

Shugaba Bola Tinubu ya takaita adadin motocin da ke ayarin Ministoci, da kananan Ministocin, da Shugabannin Hukumomin Gwamnatin Tarayya zuwa motoci uku kacal a tawagarsu ta aiki.

Fadar gwamnatin kasar ta bayyana wannan matakin rage kashe kudi a ranar Alhamis a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinsa Bayo Onanuga.

A watan Janairun wannan shekara, Shugaba Tinubu ya dauki muhimman matakai don rage kashe kudaden gwamnati, ta hanyar rage adadin mutanen da ke rakiyarsa a tafiyarsa zuwa kasashen waje daga mutum 50 zuwa mutum 20. A tafiye-tafiyen cikin gida, ya rage zuwa mutum 25.

Kazalika, ya rage tawagar Mataimakin Shugaban kasa zuwa mutum biyar a tafiye-tafiyen kasashen waje da kuma mutum 15 don tafiye-tafiyen cikin gida.

Shugaba Tinubu ya kuma umarci Mai Ba da Shawara kan Tsaron Kasa da ya tuntubi Sojoji, Hukumomin Tsaro, da sauran hukumomin tsaro na fairn kaya don tsara adadin da ya dace na motocin da za su rika bin ayarinsu.

Dandalin Mu Tattauna

Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG