Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Tinubu, Shettima A Kasa Ba Zai Haifar Da Gibin Shugabanci Ba – Fadar Shugaban Najeriya


Shugaba Tinubu, (Hagu) Shettima (Dama) (Hoto: Facebook/Kashim Shettima0
Shugaba Tinubu, (Hagu) Shettima (Dama) (Hoto: Facebook/Kashim Shettima0

Wata sanarwa da Mai bai wa Shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar ta ce shugabannin biyu “na gudanar da ayyukansu na kasa duk da cewa suna waje.

Fadar Shugaban Najeriya a ranar Laraba ta ce rashin Shugaba Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima a kasar ba zai haifar da gibi na shugabanci ba.

A ranar 2 ga watan Oktoba, Tinubu ya tafi hutu Birtaniya na makonni biyu yayin da shi kuma Shettima ya fice a kasar a ranar Laraba don halartar wani taro a Sweden.

Shettima zai wakilci Najeriya a tattaunawar hadin gwiwa da kasar ta Sweden da ke yankin kasashen Scandanavia.

"Na kama hanyar zuwa Sweden daga Abuja, inda zan kwashe kwanaki biyu wajen wakiltar Najeriya a tattaunawar hadin gwiwa da kasar ta Sweden da ke yankin kasashen Scandanavia.” Shettima ya ce a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Wata sanarwa da Mai bai wa Shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar ta ce shugabannin biyu “na gudanar da ayyukansu na kasa duk da cewa suna waje.

Onanuga ya kara da cewa dukkan bangarorin gwamnati na aiki ba tare da wata tangarda ba.

“Mun samu irin wannan yanayi a shekarar 2022 lokacin da tsohon Shugaba Buhari da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo suka kasance ba sa kasar a lokaci guda. Shugaba Buhari ya tafi taron Majalisar Dinkin Duniya na UNGA a karo na 77, yayin da Osinbajo ya halarci jana'izar Sarauniya Elizabeth I.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG