Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Jajantawa Mutanen Da Hatsarin Fashewar Tankar Mai Ya Rutsa Dasu


Bola Tinubu
Bola Tinubu

A sakon ta’aziyar da hadimin shugaban kasa Stanley Nkwocha ya fitar a yau Laraba, Shettima ya bayyana cewar, “zuciya tayi kunci saboda iyalan da wannan mummunan al’amari ya daidaita.”

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bukaci a sake nazarin ka’idojin kiyaye afkuwar hatsari yayin jigilar albarkatun man fetur a fadin Najeriya, sakamakon hatsarin fashewar tankar man da yayi sanadiyar salwantar rayuka fiye da 100 a jihar Jigawa.

A sanarwar daya fitar a yau laraba, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima a madadin Shugaba Tinubu, ya jajantawa iyalan da suka rasa masoyansu a mummunan hatsarin tare da yin addu’ar Allah ya basu hakurin jure rashin da suka yi.

A sakon ta’aziyar da hadimin shugaban kasa Stanley Nkwocha ya fitar a yau Laraba, Shettima ya bayyana cewar, “zuciya tayi kunci saboda iyalan da wannan mummunan al’amari ya daidaita.”

“Wannan mummunan hatsari yayi matukar girgizamu. Gwamnatin tarayya na tare da al’ummar jigawa. Muna yin dukkanin mai yiyuwa domin agazawa wadanda suka jikkata tare da tallafawa iyalan da iftila’in ya shafa,” a cewarsa.

Haka kuma, mataimakin shugaban kasar ya bada umarnin gaggauta tura jami’in hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) da kayan aiki zuwa jihar Jigawa.

“A yayin da muke alhinin kan afkuwar wannan bala’i, ya kamata mu sake yin duba a kan mahimmancin daukar matakan kiyaye afkuwar hatsari da wayar da kan jama’a domin kaucewa afkuwar wannan al’amari a nan gaba,” Shettima ya kara jaddadawa.

“Kowace rai tana da daraja, kuma wajibi ne muyi dukkanin mai yiuwa wajen kare al’ummarmu.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG