Majalisar Dattawa ta karbi bukatar neman tabbatar da nadin sabbin ministoci 7 da ya tura sunayensu a jiya Laraba.
Bukatar Shugaba Tinubu ta neman a gaggauta tabbatar da ministocin na kunshe ne a cikin wasikar daya aikewa Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio wanda ya karantata a farkon zaman majalisar na yau Alhamis.
Tinubu ya bukaci majalisar ta yi nazari tare da tabbatar sunaye 7 da ya nada a matsayin ministoci.
Ministocin da ake neman a tabbatar din sun hada da Nentawe Yilwatda ta ma’aikatar jin kai da rage talauci, da Muhammad Maigari Dingyadi na ma’aikatar kwadago da ayyukan yi da, Bianca Odumegwu-Ojukwu karamar minista a ma’aikatar kasashen waje da kuma Jumoke Oduwole ta ma’aikatar masana’antu, ciniki da zuba jari.
Sauran sun hada da Idi Mukhtar Maiha na ma’aikatar bunkasa kiwon dabbobi, da Yusuf Ata, karamin minista a ma’aikatar gidaje da raya birane sai kuma Suwaiba Ahmad, karamar ministar ilimi.
Akpabio ya mika sunayen ga babban kwamitin majalisar domin kammala ayyukan majalisa akansu ba tare da bata lokaci ba.
Dandalin Mu Tattauna