Najeriya dai na fama da matsalar tsadar kayan abinci sakamakon matsalolin da suka hada da cire tallafin man fetur da rashin tsaro.
Sai dai a wani mataki na dakile matsalar, Ministan Yada Labarai da Wayar da kan al’ummar Najeriya, Muhammad Idris, ya bayyana cewar Tinubu ya umarci shugabannin hukumomin tsaro da mashawarcinsa akan harkokin tsaro su hada kai da gwamnonin jihohi domin lalubo bakin zaren.
A jawabin ministan bayan kammala taron gaggawa tsakanin Shugaba Tinubu da gwamnonin jihohin Najeriya a Alhamis din nan, “da fari dai, an umarci babban sufetan ‘yan sandan najeriya da Darakta Janar Na Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS su hada kai da gwamnonin jihohi wajen warware matsalar masu boye kayan masarufi.”
“A dai dai wannan gaba da al’ummar kasar nan ke bukatar wadatar abinci domin shawo kan matsalar hauhawar farashi tare da samawa ‘yan Najeriya abinda zasu kai bakin salatinsu, wasu ‘yan kasuwa na amfani da wannan dama wajen boye kayan abinci da nufin gallazawa jama’a tare da samun kazamar riba sakamakon hakan.”
“Don haka, gwamnoni da Shugaban Kasa sun dauki wannan matakin cewa hukumomin tsaro su hada kai da gwamnonin jihohin domin kawo karshen matsalar.”
Shugaba Tinubu ya bada umarnin samar da hatsi domin shawo kan hauhawar farashin kayan masarufi a yayin da gwamnatin tarayya ke duba yiyuwar shigo da kayan abinci daga ketare.
Sai dai Minista Idris yace a halin yanzu an jingine wannan batu.
A cewar sa, “an kuma dauki mataki domin kare muradan kasarmu, babu bukatar shigo da abinci daga ketare a halin yanzu. Najeriya na iya ci da kanta harma ta zamo me fitar da shi zuwa wasu kasashen.”
“Bama son maida hannun agogo baya game da irin ci gaban da muka samu akan noman abinci a kasarnan. Halin da muke ciki yanzu wahala ce ta dan wani lokaci kuma zata gushe nan bada jimawa ba.”.
Dandalin Mu Tattauna