Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sha alwashin magance wahalhalun da ake fama dasu a halin yanzu, musamman hauhawar farashin kayan abinci da magunguna a fadin kasar ta hanyar kaddamar da kamfanin bada lamuni na kasar
A sakonsa na murnar shiga sabuwar shekarar 2025 ga 'yan Najeriya a yau Laraba, gwamnatin tarayyar kasar tace matakin zai bunkasa sarrafa muhimman magunguna da sauran bukatun kiwon lafiya a cikin Najeriya a sabuwar shekarar.
A cewar shugaban kasar, ana sa ran sabon kamfanin ya fara aiki kafin karshen zango na 2 na sabuwar shekarar, kuma hadin gwiwa ne tsakanin hukumomin gwamnatin da suka hada da bankin raya masana'antu (BOI) da hukumar baiwa masu sayen kaya lamuni ta Najeriya (NCCC) da hukumar bunkasa kadarorin gwamnatin najeriya (NSIA) da ma'aikatar kudin kasar da bangaren kamfanonin masu zaman kansu da kuma kamfanonin kasa da kasa.
A cewar shugaban kasar, "a yayin da sabuwar shekarar ke kamawa, ta shigo tare da dimbin fata da buri, da kuma hasashen kyautatuwar al'amura. Da yardar Allah shekarar 2025 za ta zamo mai cike alwashin cikar burakanmu”
Dandalin Mu Tattauna