A sakonsa na murnar shiga sabuwar shekara ga 'yan Najeriya musamman ma ma'aikata, shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, ya ce bukatar janye kudurorin ta taso ne bisa la'akari da walwalar ma'aikatan Najeriya.
Ya kuma yi tsokaci game da bukatar gwamnati ta rika gudanar da lamuranta a bayyane da yin tafiya da kowa da kuma nuna halayyar gaskiya a mu'amalarta da talakawa.
"A yayin da muke shiga 2025, kungiyar kwadago ta NLC, na mika sakon gaisuwar shiga sabuwar shekara ga ilahirin ma'aikata da al'ummar kasarmu Najeriya.
Dandalin Mu Tattauna