Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Ana Ci Gaba Da Ce-ce-ku-ce Kan Samar Da ‘Yan Sandan Jihohi


Sufeta Janar Na ‘Yan Sandan Najeriya Lokacin Da Ya Jagoranci Taron Samar Da Tsaro
Sufeta Janar Na ‘Yan Sandan Najeriya Lokacin Da Ya Jagoranci Taron Samar Da Tsaro

Batun samar da ‘yan sanda mallakar gwamnatocin jihohi a Najeriya na ci gaba da janyo tabka muhawara a tsakanin ‘yan kasar da yawansu ya haura sama da milyan dari biyu

Ya zuwa karshen shekara ta 2024 da ta kare Najeriya dai na da yawan ‘yan sanda dubu dari hudu(400,000) lamarin da masana harkokin tsaro suka ce sun yi kadan wajen baiwa al'umma da ma dukiyoyinsu kariya,

Tuni dai masu ruwa da tsaki da suka hada kungiyoyin addini da na kare hakkin dan adam suka fara yin tsokaci a kan lamarin,

Shugaban Majalisar Dokokin jihar Neja Barista Abdulmalik Sarkin Daji ya ce samar da ‘yan sandan jihohin zai taimaka wajan rage barna da rashin tsaro da ya addabi kasar.

Suma dai shugbannin addinai sun bayyana cewa samar da ‘yan sandan jihohin ya na da muhimmanci wajen samar da tsaro ga kasar.

Sheik Abdullahi Bala Lau shugaban kungiyar Izala mai wa’azin Musulunci a Najeriya ya ce idan an bi tsarin da yakamata tabbas zai taimakawa jami’an tsaron da ake dasu yanzu.

Tsohon Mataimakin shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN a yankin Arewacin Najeriya Rabaran Musa S. Dada ya ce ko da yake lamarin yana da amfani amma dai yana da dan shakku kar wasu su hana su aikin da yakamata.

Shugaban kungiyar kare hakkin ‘dan Adam a jihar Neja Kwamred Abubakar Abdullahi ya ce suma suna da irin wannan shakku.

Tsohon mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya AIG Suleman, Gwamna mai ritaya ya na mai cewa babu wata damuwa ga samar da ‘yan sandan jihohin domin ko ‘yan sandan da ake da su yanzu kusan suna samun tallafi ne daga gwamnatocin jihohin.

A yanzu dai ‘yan Najeriya na cike da fatar samun mafita a kan matsaloli na rashin tsaro da suka addabi bangarori da dama na kasar.

Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasir Batsari:

Ce-ce-ku-ce Kan Batun Samar Da ‘Yan Sanda Mallakar Gwamnatocin Jihohin Najeriya.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:33 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG