WASHINGTON DC - A jawabinsa bayan taron, Shugaban kasar na cewar, "da fari, wajibi ne in yabawa 'yan Majalisar Dokokinmu na kasa saboda yadda suka hanzarta zartar da wannan kudiri da yayi la'akari da yaran Najeriya, wanda ya fahimci cewar ilimi ne makamin daya fi dacewa a yaki talauci da shi."
"Mun kudiri aniyar tabbatar da cewar ilimi ya samu kulawar data dace a kasar, ciki harda tsare-tsaren bunkasa sana'o'in hannu. Za'a yi hakan domin tabbatar da cewar ba'a tauyewa kowa hakkinsa na samun ingantaccen ilimi da gina nagartacciyar rayuwa ba komin talaucinsa".
"Muna wannan mataki ne saboda mun samu ilmi kuma an taimaka mana. A da, mun ga yadda dinbim yaranmu suka bar makaranta suka sarayyar da damar. Hakan ta kau a yanzu, akwai ka'idoji da zaka bi domin neman wannan dama matukar kai dan najeriya ne."
Game da batun biyan bashin, dokar ya nuna cewar mutum zai fara biyan bashin ne da zarar ya samu aiki kowane iri ne.
A cewar bayanan dokar, asusun ba zai fara shirin karbar bashin ba har sai bayan shekaru 2 da kammala aikin hidimar kasa.
Bayanan sun kara da cewar, wanda ya ci gajiyar rancen na iya neman karin wa'adi ta hanyar yin rantsuwa a kotu cewar bai samu aiki kowane iri ba kuma baya samun kudin shiga ta ko ina.
Haka kuma bayanan sun yi nuni da cewar duk wanda ya baiwa asusun bayanan bogi karkashin wannan sashe ya aikata laifin cin amanar kasa wanda hukuncinsa zaman gidan kaso ne tsawon shekaru 3.
Har ila yau bayanan sun yi tanadin yafe bashin idan mutum ya mutu ko ya samu nakasar da zata iya hana shi biyan bashin.
A wasikar daya aikewa Majalisar Dattawan Najeriya Shugaba Bola Tinubu ya bukaci a soke dokar da ake amfani da ita tare da maye gurbinta da sabon kudirin daya ke son a zartar a matsayin doka.
A watan Yunin bara Tinubu ya rattaba hannu akan kudirin dokar rancen dalibai domin baiwa daliban Najeriya damar samun rancen da babu kudin ruwa a cikinsa.
Saurari bidiyon lokacin da Shugaban ya sanya hannu kan dokar a fadar gwamnatin tarayyar Najeriya ta Aso Rock
Dandalin Mu Tattauna