Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Haramtawa Ministoci Tafiye-tafiye Zuwa Ketare


Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu

A wani babban mataki na rage kudaden da ake kashewa, Shugaba Bola Tinubu ya sanya dokar hana tafiye-tafiye na tsawon watanni uku zuwa kasashen waje da ake amfani da kudaden gwamnati ga duk Ministoci, Shugabannin hukumomin gwamnati, da sauran jami’ai.

Haramcin, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Afrilu, 2024, an yi shi ne don rage yawan amfani da kudade da ma’aikatu, sassan gwamnati, da hukumomi ke kashewa kan tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da kuma tabbatar da cewa ma’aikatan sun mai da hankali kan ayyukan da ya rataya a kansu.

Haramcin ya zo ne cikin wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Hon. Femi Gbajabiamila da sakataren gwamnatin tarayya George Akume wadda aka sanya wa hannu a ranar 12 ga watan Maris din 2024.

Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Najeriya Femi Gbajabiamila
Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Najeriya Femi Gbajabiamila

Wasikar haramcin ta kara da cewa, “Shugaban kasa ya damu da almabazzarancin da ke kunshe da tafiye-tafiyen jami’ai da sauran hukumomin gwamnati, da kuma bukatar da ke akwai ta mambobin Majalisar ministoci da shugabannin MDA na su mai da hankali kan ayyukansu na cikin gida maimakon balaguro”

Wasikar ta ce “Bisa la’akari da kalubalen tattalin arziki da ake fuskanta a halin yanzu da kuma bukatar gudanar da harkokin kasafin kudi, na rubuto ne domin in isar da umarnin shugaban kasa na sanya dokar hana fita na wucin gadi ga dukkan jami’an gwamnatin tarayya a dukkan matakai har na tsawon watanni uku daga Afrilu 2024.”

Tinubu ya kara da cewa, daga yanzu jami’an gwamnati da ke da niyyar tafiya duk wata ziyarar aiki a kasashen waje dole ne su nemi amincewar shugaban kasa akalla makonni biyu kafin su fara shirin tafiyar, kuma fadar Shugaban za ta amince ne da tafiyar kawai idan ta zama dole.

Idan ba a manta ba, a watan Janairu ne shugaba Tinubu ya ba da umarnin rage yawan tawagar masu yi masa rakiya da na mataimakinsa a tafiye-tafiyen cikin gida zuwa 25 da kasashen waje zuwa mutum 20 kacal.

Sai dai duk da hakan Shugaban ya gamu da kakkausar suka bayan tawagar mutane 590 sun yi masa rakiya zuwa birnin Dubai na hadaddiyar Daular Larabawa yayin taron yanayi na COP28, ko da ya ke gwamnatin ta ce mutane 422 kadai ta dauki nauyin balaguron na su.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG