Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Zartarwa Ta Tarayya Ta Amince Da Aiwatar Da Rahoton Oronsaye, Na Hade Hukumomi A Wuri Guda   


Shugaba Bola Ahmed Tinubu (Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu)
Shugaba Bola Ahmed Tinubu (Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu)

Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da aiwatar da wani sashe na rahoton kwamitin Stephen Orasanye kan hada wasu hukumomin da ma'aikatun gwamnati a wuri guda, a yayin da wasu kuma za'a sauya musu fasali ko kuma a rushesu sannan wasu kuma a sauya musu matsugunai.

An cimma wannan matsaya ne a yayin zaman Majalisar Zartarwa da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a yau Litinin.

Hakan, a cewar Hadimar Shugaban Kasar akan Aiwatar da Manufofi, Hadiza Bala Usman, ya dace da bukatar rage kashe kudade wajen gudanar da gwamnati tare da inganta kwazo a dukkanin matakan aikin gwamnati.

Haka kuma, Majalisar Zartarwa ta karbi rahoton Kwamitin Alaka Tsakanin Ma'aikatun Gwamnati da aka kafa domin sake nazarin tallafawa al'umma na kasa.

Har ila yau, Majalisar Zartarwa ta amince da sake farfado da shirin baiwa iyalai miliyan 12 tallafin kudade kai tsaye da suka kunshi 'yan Najeriya miliyan 60 dake da matukar bukata.

A shekarar 2011, Shugaban Kasar wancan lokacin Goodluck Jonathan, ya kafa kwamitin sauya fasali da daidata hukumomi da ma'aikatun gwamnati karkashin jagorancin Oransaye.

A ranar 16 ga watan Afrilun shekarar 2012, kwamitin ya gabatar da wani rahoto mai feji 800 da ya tantance dimbin hukumomin da ayyukansu ke kamance da juna abinda ke haddasawa gwamnati asara wajen kashe kudade.

A cewar rahoton akwai hukumomi da ma'aikatun gwamnati 541, tare da bada shawarar rage hukumomi 263 su koma 161, a rushe 38 a kuma hada 52 a wuri guda.

An samu gabatar da kuduriri ba tare da aiwatar da wani abin a zo a gani ba karkashin shekaru 8 na Shugaban Kasa Muhammad Buhari, saidai aiwatar da rahoton yayi daidai da muradan sabuwar gwamnatin da ta gajeshi a kokarinta na rage yawan kashe kudade.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG