Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Bada Umarnin Sake Bude Kan Iyakokin Najeriya Da Jamhuriyar Nijar Ta Sama Da Kasa


Iyakar Najeriya da Nijar
Iyakar Najeriya da Nijar

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bada umarnin gaggauta bude kan iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar. Haka kuma, ya umarci a janye dukkanin takunkuman da aka kakabawa kasar nan take.

WASHINGTON DC - Sanarwar da hadimin shugaban kasar akan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar tace, umarnin na zuwa ne a matsayin wani bangare na aiwatar da shawarwarin da taron shugabanin kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), daya gudana a ranar 24 ga watan Fabrairun daya gabata a birnin Abuja.

Haka kuma, Tinubu ya janye dukkanin dakatarwar da aka yiwa harkokin kasuwanci da hada-hadar kudi tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, ciki harda dakatarwar da aka yiwa kayayyakin more rayuwa da wutar lantarki daga zuwa Nijar.

Shugaban Najeriyar ya kuma bada umarnin sakin dukkanin kudaden Jamhuriyar Nijar dake taskance a manyan bankunan kasashen ecowas.

Sanarwar ta kara da cewar, "an janye dukkanin haramcin tafiye-tafiye da aka kakabawa jami'an gwamnatin Nijar da iyalansu".

Haka kuma, an mika makamancin wannan karamci ga kasar Guinea, ta hanyar janye takunkumai akan hada-hadar kudi da tattalin arziki.

Idan ba'a manta ba shugabann kungiyar ECOWAS sun amince su janye takunkuman karya tattalin arziki da suka kakabawa kasashen Nijar, Mali, Burkina Faso da Guinea.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG