Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Timileyin Ajayi Ya Ki Ya Amsa Laifin Kisan Salome Adaidu


Ana tuhumarsa ne da laifi guda na kisan kai wanda hukuncin sa kisa ne, wanda ya saba da sashe na 221 kundin “penal code”, na hukunta manyan laifuffuka a arewacin Najeriya.

An gurfanar da, Timileyin Ajayi, mutumin da ake zargi da kisan Salome Adaidu, a gaban babbar kotun Nasarawa, dake zamanta a Lafiya, babban birnin jihar.

Ana tuhumarsa ne da laifi guda na kisan kai wanda hukuncin sa kisa ne, wanda ya saba da sashe na 221 kundin “penal code”, na hukunta manyan laifuffuka a arewacin Najeriya.

A yau Litinin ne aka gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Simon Aboki, kuma da gurfanar tasa, wanda ake tuhumar ya ki amincewa da aikata laifin da ake zarginsa da aikatawa

An kama wanda ake zargin mai shekaru 32 ne bisa zarginsa da hallaka budurwarsa, Adaidu, ‘yar hidimar kasa mai shekaru 24, wacce tayi aikin hidimar kasar tare da nicon insurance dake birnin tarayyar Najeriya, Abuja, gabanin mutuwarta.

An kama Timi ne a ranar Lahadi, 12 ga watan Janairun da muke ciki, sa’ilin da yake kokarin wurgar da kan Salome bayan daya kashe tare da daddatsa naman jikinta lokacin da ta kai masa ziyara a gidansa.

Da yake amsa tambayoyi a wata kebabbiyar hira da tashar talabijin ta Channels, wanda ake zargin yayi ikrarin kisan Salome, inda yace ba tsararren al’amari bane saidai saboda basa samun lokacin juna a ko da yaushe.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG