Majiyoyin tsaro da mazauna garin Malam Fatori a jiya Lahadi, sun ce wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu ikirarin da’awar kishin Islama ne, sun kashe sojojin Najeriya a kalla 20, ciki har da wani kwamanda, bayan wani harin da suka kai wani sansanin soji a wani yanki dake dan lungu a Jahar Barno a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Mayakan Boko Haram da na ISIS Shiyyar Afurka Ta Yamma (ISWAP), sun fi gudanar da harkokinsu a jahar ta Borno, inda suke auna jam’an tsaro da farar hula, wanda ta haka su ka hallaka tare da kawar da dubban mutane.
Harin na baya bayan nan ya auku ne ranar Jumma’a, lokacin da mayakan ISWAP su ka zo cikin motoci masu bindigogi, su ka far ma Bataliya ta 149 ta sojojin Najeriya da ke garin Malam-Fatori, wanda ke kan hanyar zuwa kan iyakar Nijar, a cewar wasu sojoji biyu da mazauna wurin.
Wani soja da ya tsallaka rijiya da baya, ya fada wa wakilin Reuters ta wayar tarho cewa, ‘yan ta’addan sun sammaci dakarun ne inda suka” bude musu wuta ta ko ina.”
“Mun yi iya kokarin mu don kare kan mu sannan bayan sa’o’I uku muna dauki ba dadi da su, daga baya suka yi galaba akan mu sannan sun kashe kwamandan mu mai mukamin Laftanar Kanar, inji wani soja da ya nemi a sakaya sunan shi don ba a bashi izinin magana da ‘yan jarida ba.
Reuters ta nemi jin ta bakin wani mai Magana da yawun sojojin Najeriya amma bai ce uffan ba nan take.
Mazauna garin da suka kaurace sun ce an ga wasu ‘yan ta’addan a garin Malam -Fatori a daren ranar Asabar.
Dandalin Mu Tattauna