Zababben shugaban kasa Donald Trump ya ce akwai alamun zai bai wa TikTok Karin kwanaki 90 daga yiwuwar dakatar da shi bayan ya hau kan karagar mulki a ranar Litinin, alkawarin da TikTok ya nakalto a wata sanarwa da ya wallafa ga masu amfani da manhajar.
TikTok, mallakin kamfanin ByteDance na China, ya gayawa masu amfani da ke kokarin amfani da manhajar da misalin karfe 10:45 agogon ET, wato karfe 3:45 agogon GMT, abin takaici an kafa dokar hana amfani da TikTok a Amurka, wannan yana nufin ba za ku iya amfani da TikTok a yanzu ba.
“Mun yi sa’a cewa shugaba Trump ya nuna cewa zai yi aiki tare da mu kan hanyar da za a sake dawo da TikTok da Zarar ya hau kan karagar mulki. Da fatan za’a saurare mu.”
Sauran manhajoji mallakar ByteDance, da suka hada da manhajojin Capcut da Lemon8, suma sun daina aiki kuma babu su a shagunan manhaja na Amurka har zuwa maraicen ranar Asabar.
Trump ya shaida wa gidan talabijin na NBC a wata hira cewa, "wasu karin kwanaki 90 wani abu ne da za’a iya yi, domin abu ne da ya dace." "Idan na yanke shawarar yin hakan, tabbas zan sanar a ranar Litinin."
Sai dai ba a bayyana ko wasu masu amfani da shi a Amurka za su iya shiga manhajar din ba, amma baya aiki ga mafi yawan masu amfani kuma mutane da suke ta kokarin shiga ta manhajar ta hanyar yanar gizo suna cin karo da sako iri daya cewa TikTok baya aiki.
Dandalin Mu Tattauna