Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya ce "akwai alamun" zai bai wa TikTok karin kwanaki 90 daga yiwuwar dakatar da shi bayan ya hau kan karagar mulki a ranar Litinin, yayin da manhajar da ke da masu amfani da ita Amurkawa miliyan 170, ta ke cike da fargaba gabanin rufe ta da aka tsara yi a ranar Lahadi.
Trump ya shaida wa gidan talabijin na NBC a wata hira cewa, "wasu karin kwanaki 90 wani abu ne da za’a iya yi, domin abu ne da ya dace." "Idan na yanke shawarar yin hakan, tabbas zan sanar a ranar Litinin."
Manhajar mallakar kasar China, wacce ta ja hankalin kusan rabin Amurkawa, ta karfafa kananan sana'o'i da kuma tsara al'adun yanar gizo, ta fada a ranar Juma'a cewa za ta rufe a Amurka a yau Lahadi, sai dai idan gwamnatin shugaba Joe Biden ta ba da tabbaci ga kamfanoni irin su Apple da Google cewa, ba za su fuskanci tsaurarawa ba a lokacin da haramcin ya fara aiki ba.
A karkashin wata doka da aka zartar a shekarar da ta gabata, wadda kotun koli ta amince da ita bai daya a ranar Juma'a, dandalin na da wa'adin zuwa yau Lahadi da ya yanke hulda da uwar kamfaninsa na kasar China, ByteDance, ko kuma ya dakatar da ayyukansa na Amurka, don warware damuwar da ake da ita na cewa tana barazana ga tsaron kasa.
Fadar White House ta yi watsi da kalaman TikTok na ranar Juma'a a matsayin wani abin al'ajabi, tare da nanatawa a ranar Assabar cewa, ya rage ga gwamnatin Trump mai zuwa ta yi wani abu a kai, lamarin da ya kara jaddada yiwuwar rufe ta a yau Lahadi.
Sakatariyar yada labarai Karine Jean-Pierre ta ce "Ba mu ga dalilin da zai sa TikTok ko wasu kamfanoni za su dauki mataki nan da 'yan kwanaki masu zuwa ba kafin gwamnatin Trump ta hau karagar mulki a ranar Litinin."
TikTok bai amsa nan take ba ga bukatar yin tsokaci kan sabuwar sanarwar fadar White House.
Dandalin Mu Tattauna