Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Nemi Kawo Karshen Zaman Doya da Manja Tsakanin Bakake da 'Yansanda


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Kwana daya bayan jadada cewa kawunan Amurkawa basu rarrabu ba kamar yadda wadansu ke harsashe, shugaban Amurka Barack Obama zai gana da jami’an tsaro, da shugabannin kungiyoyin kare hakin bil’adama, da ‘yan fafatuka, da shugabannin siyasa, domin tattaunawa kan hanyoyin da za a maido da yarda tsakanin al’ummomi dake zaman doya da manja tsakanin ‘yan sanda da mazauna yankunan da suka dauki rantsuwar karewa.

Ganawar da za a yi yau Laraba fadar White House, ta biyo bayan jawabin da shugaba Obama ya yi jiya a wajen taron tunawa da ‘yan sanda biyar da aka kashe a Dallas, inda yace tashin hankalin da aka fuskanta makon da ya gabata, ya nuna irin “matukar tsatsaguwa da aka samu a damokaradiyarmu”.

Hotunan 'yansandan da aka kashe a Dallas
Hotunan 'yansandan da aka kashe a Dallas

Harin da wani tsohon soja, Bakar Fata, ya kaiwa ‘yan sanda a Dallas sakamakon kashe wadansu bakaken fata biyu da aka yi a jihohin Louisiana da Minnesota ya kara zafafa muhawara kan wariyar launin fata da jami’an tsaro ke nunawa.

A cikin jawabinsa da ya tabo batun mika wuya da kwazo da jami’an tsaro ke nunawa a gudanar da ayyukansu, da batun nuna wariyar launin fata a Amurka, Obama yace ya fahimci cewa al’ummar Dallas da da sauran 'yan kasar duk suna wahala.

Shugaba Obama ya kuma karrama jami’an yan sanda biyar din da aka kashe da ya kuma yi kira da a sami hadin kai da kyakkyawan fatar makoma mai kyau.

XS
SM
MD
LG