Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama Ya Karrama 'Yansanda Biyar Da Aka Kashe A Dallas


Shugaban Amurka Barack Obama ya karrama 'jami'an 'yansandan nan biyar da aka kashe a wata hidimar tunawa da su da aka yi a Dallas, inda ya ce tashin hankalin makon da ya gabata ya fallasa "babbar matsalar nan da ke tattare da tsarin Demokaradiyyarmu" amma ya jaddada cewa kasar ba ta rabu kamar yadda wasu ke ikirari ba.

Shugaban na Amurka ya shawarci Amurkawa da su kokarta su cimma jituwa, a daidai lokacin da ya ke famar hada kan kasar da tayi matukar rabuwa kan abubuwan da su ka shafi dangantakar jinsi tsakanin jami'an tsaro da kuma tsirarun al'ummomin da suke wa aiki.

Harin da wani tsohon soja Bakar fata ya kai kan 'yansandan Dallas saboda harzukar da yayi da kashe wasu Bakar fata biyu da 'yan sandan suka yi a Lousiana da Minnesota ya dada zafafa muhawarar da ake yi kan batun nuna wariya a bangaren jami'an tsaro.

A jawabin nasa, wanda ya tabo batutuwa,kama daga kan jinjinawa jami'an tsaro, zuwa wariyar launin fata, Obama yace ya fahimnci cewa jama'a a fadin Dallas da ma kasar baki daya na cikin bakin ciki.

Shi kuwa Magajin Garin Dallas Mike Rawlings cewa ya yii "yansandan ma'abuta zaman lafiya ne da suka mutu cikin kaki; sun mutu ne saboda wannan sadaukar da kai da suka yi" ya kara da cewa, "An taba zuciyar wannan birni namu, lokacin da aka yi masu kwantan bauna ta salon raganci," Ya kara da cewa "yau dole ne mu yi batun hadin kai."

Mataimakin Shugaban Kasa Joe Biden da kuma Shugaban da Obama ya gada, tsohon Shugaban kasa George W. Bush, su ma sun hallara.

Bush ya yi Allah wadai da abin da ya kira, "kiyayya da gaba" da suka janyo kashe-kashen, sannan ya yi kiran da a hada kai, a nuna karfin gwiwa da hakuri da juna bayan wannan al'amarin. Tsohon Shugaban na Amurka ya yi kira ga Amrkawa da su mutunta abin da ya kira, "Surar Allah da mu kan gani a juna."

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG