Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TG Omori Na Fama Da Ciwon Koda


TG Omori (Hoto: Facebook/ TG Omori)
TG Omori (Hoto: Facebook/ TG Omori)

Omori ya ba da umarni a daukan bidiyon wakoki sama da 200 ciki har da na fitattun mawakan Najeriya irinsu Davido, Fire Boy da Ashake.

Rahotanni a Najeriya na cewa fitaccen Darektan hada bidiyon wake-wake ThankGod Omori, wanda aka fi sani da TG Omori na kwance a asibiti yana fama da ciwon koda.

A wani sakon Twitter da ya wallafa a ranar Asabar, Omori ya ce daya daga cikin kodojinsa ta daina aiki.

“Shekara daya bayan da kodata guda daya ta daina aiki, an yi min dashen koda amma aikin bai yi ba.” Omori ya ce a shafinsa na X.

Ya kara da cewa, “dan uwana daya da nake da shi ya ba ni daya daga cikin nasa don na rayu.”

A cewar Omori, sau uku ana yi masa aiki kan wannan rashin lafiya.

A ‘yan kwanakin bayan ne Omori ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa, “ba na so na mutu.”

Omori ya ba da umarni a daukan bidiyon wakoki sama da 200 ciki har da na fitattun mawakan Najeriya irinsu Davido, Fire Boy da Ashake.

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG