Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Bikin Auren Gargajiyar Davido Da Chioma Cikin Kasaita


Davido da Chioma
Davido da Chioma

Bikin na ranar Talata ya zo ne kimanin makonni biyu bayan da Davido ya tabbatar da aurensa da Chioma.

A ranar Talata ne aka gudanar da shagalin bikin auren fitaccen mawakin Afrobeat Davido Adeleke da dadaddiyar budurwarsa Chioma Rowland a wani kasaitaccen bikin auren gargajiya a birnin Legas da ya samu halarta ‘yan masana’antar nishadantarwa da wasu manyan baki.

Taron bikin, wanda aka gudanar a Harbor Point da ke yankin Victoria Island a jihar Legas, ya nuna shekarun da suka shafe suna soyayya, kuma kamar yadda ake sa ran bikin ya karade shafukan sada zumunta.

Bikin na ranar Talata ya zo ne kimanin makonni biyu bayan Davido da ya tabbatar da aurensa da Chioma.

Davido Da Chioma
Davido Da Chioma

Hotunan bikin sun karade shafukan sada zumunta yayin da masoya, fitattun mutane, sarakunan gargajiya da ‘yan siyasa suka taya ma’auratan murna.

Masoya da mashahuran mutane sun yi ta yada hotuna da bidiyo daga bikin, inda su ke taya sabbin ma’auratan murnar auransu.

Kamar yadda aka zata, auren Davido za’a samu halartar manyan baki daga sassan daban-daban na rayuwa.

Davido da Chioma
Davido da Chioma

Daga cikin wasu manyan bakin da suka halarci taron bikin Davido da Chioma sun hada da Ooni of Ife Oba Adeyeye Ougnwusi, Victor Osimhen; tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom Udom Emmanuel; tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo; Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki; da takwarar aikinsa na ona Ogun Dapo Abiodun; Sanata Daisy Danjuma, mai wakiltar Edo ta Kudu.

Abotar Chioma da Davido ta samo asali ne tun shekaru da dama da suka gabata. Amma a shekarar 2018 ne mawaki ya tabbatar da soyayarsu a wani taron jama’a a watan Oktoba na 2018.

Har ila yau Davido ya gwangwaje amaryarsa Chioma da wata sabuwar mota a ranar Talata.

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG