TASKAR VOA: Cire tallafin mai a Najeriya ya haifar da tashin farashin abubuwa da dama, yanzu mutane su na daukan matakan rage kashe kudi
Halin matsin tattalin arziki a Najeriya sakamakon cire tallafin man fetur ya sa hukumomin yin kokarin bunkasa amfani da wasu hanyoyin makamashi da ba na fetur ba, abin da ya hada da canza injuna zuwa masu aiki da iskar gas da fadada tashoshin cajin motoci masu amfani da lantarki, da wasu rahotanni