Shugabannin al’ummar Hausawa mazauna Legas a Najeriya sun ja hankalin direbobi masu dakon kaya daga kudu zuwa arewa, bayan 'yan sanda sun kama wasu mutane a Legas ne da tarin alburusai a wasu motocin bas, wadanda aka yi nufin kai su Katsina, da wasu rahotanni.