Kyauta a tsakanin samari da 'yan mata na taka rawar gani wajan kara dankon zumunci tsakanin masoya a cewar wasu daga cikin 'yan matan da muka sami zantawa da su.
Koda shike wasu 'yan matan sunce yawancin samaroi masu bada kyautar ba suna badawa saboda so bane kawai, sun kara da cewa wasu samarin sukan kiga duk abin da suka bada domin daga karshe idan suka gane ba'ayi da su, sai su koma su ce sai an biya su duk abin da suka kashe ma yarinyar.
Babbar matsalar ma itace wasu samarin sukan bada kyautar ne domin su nemi wani abu daga jikin budurwar ta su a madadin kyautar da suke ba 'yan matan wato abin ya zama tamkar bani gishiri in baka manda kenan.
Kyauta bata karanta, dan haka 'yan mata da dama sun nuna ra'ayin su akan amincewa da samari masu bada kyauta.
A tambayar da dandali yayi dangane da goyon bayan iyaye musamman dangane da amsar kyauta daga wurin samarin, yawanci sun nuna cewar koda sun koma da kyautar kaya ko wasu abubuwa masu nasaba da samarin su, suna da hanyoyi da dama na yi ma iyayen su karya.
Saurari cikakken shirin anan.