A wani taronmasu ruwa da tsaki na jihar da aka yi karkashin jagorancin gwamna Umaru Tanko al-Makura, a Lafia, babban birnin Jihar, gwamnati ta tabbatarwa da jama'a cewar ba zata yi kasa a guiwa ba wajen hukumta wadanda suka kashe jama'a, ciki har da kisan da aka yi ma jami'an tsaro, wanda kuma ake dora laifinsa a kan wata kungiyar asiri ta kabilar Eggon mai suna Ombatse.
Wakiliyar Sashen Hausa, Zainab Babaji, ta ambaci gwamna al-Makura na Jihar ta Nassarawa yana fadin cewa yanzu dai kura ta lafa a rikice-rikicen, sai dai akwai sauran rina a kaba, domin har yanzu ba a kamo an hukumta wadanda suka kashe jami'an tsaro a Alaki ba.
Ya lashi takobin cewa ko ba dade ko ba jima, sai gwamnatinsa ta farauto wadanda suka aikata wannan kisa ta hukumta su, domin ya zamo hannunka mai sanda ga duk wani mai tunanin tayar da fitina a cikin jihar ko bata mata suna.
Sai dai kuma, wannan taron baki dayansa ya bayyana bacin rai da takaicin yadda ministan yada labarai Labaran Maku, da sanata Solomon Ewuga da kuma tsohon gwamnan Jihar ta Nassarawa, Aliyu Doma, suka ki zuwa wurin wannan taron.
Ga rahoton Zainab babaji daga Lafia...